1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa rundunar shirin ko-ta-kwana a Nijar

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 10, 2023

Kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO, ta amince da fara hada rundunar musamman ta shirin ko-ta-kwana domin mayar da gwamnatin da sojoji suka kifar a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/4V17t
Najeriya | Abuja | ECOWAS | CEDEAO | Nijar | Juyin Mulki
Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, za ta kafa rundunar musamman ta shirin ko-ta-kwanaHoto: Gbemiga Olamikan/AP/picture alliance

Matakin na kunshe cikin sanarwar bayan taron da kungiyar ta Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO, ta kammala a Abuja fadar gwamnatin Najeriya. Kungiyar ta ce ta dauke wannan matakin ne, bayan duk wani yunkuri na shawo kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar din ya ci tura. Tun da fari a jawabinsa na kammala taron shugaban Najeriya kana jagoran kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, babu wani mataki da kungiyar ba za ta dauka ba har da amfani da karfin soja da suke fatan ya zama mataki na karshe.