ECOWAS na neman dubban miliyoyi domin yaki da ta'addanci.
June 27, 2024Kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin Afirka ECOWAS za ta bukaci dala biliyan biyu da miliyan 600 a duk shekara domin kafa wata gagarumar rundunar tsaro mai mayaka dubu biyar da nufin yaki da ta'addanci. Wannan guda ne daga cikin hanyoyin da taron ministocin tsaro da na kudi na kasashe mambobin kungiyar da ke taro a Abujar Najeriya ya bayyana da ranar yau.
Kasashen yammacin na Afirka mai fama da juye-juyen mulki, a hannu guda na fuskantar rigingimun siyasa da ke bukatar hannu da yawa. Cikin watan Janairu ne kasashen Nijar da Burkina Faso gami da Mali wadanda sojoji ke jan gwamnatocinsu, suka bayyana ficewa daga ECOWAS din mai kasashe 15 mambobi.
Sojojin da suka kwace iko a kasashen uku dai, duk sun zargi gwamnatocin farar hula ne da bai wa kungiyoyin ta'adda damar sheke aya a kasashen.