1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugabannin ECOWAS sun dakatar da Burkina Faso

Suleiman Babayo ATB
January 28, 2022

Yayin taron gagga da ya gudana kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS/CEDEOA ta dakatar da Burkina Faso sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

https://p.dw.com/p/46EiT
Burkina Faso I Col. Henri Sandaogo Damiba
Hoto: Sophie Garcia/AP/picture alliance

A wannan Jumma'a bungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS/CEDEOA ta dakatar da kasar Burkina Faso sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar ranar Litinin da ta gabata inda suka kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Roch Marc Christian Kabore kuma suke ci gaba da tsare shi.

Yayin taron da shugabannin suka yi na tsawon sa'oi uku, sun kuma yanke matakin tura wata tawoga zuwa kasar ta Burkina Faso ranar Asabar.

Tun farko a wannan Alhamis da ta gabata, sabon jagoran mulkin sojan kasar Burkina Faso, Laftanar Kanar Paul-Henri Damiba ya ce kasar da ke yankin yammacin Afirka za ta koma tafarkin dimukaradiyya lokacin da ya dace bayan kawar da mastalolin da kasar ta samu kanta da suka janyo aka kifar da tsohon Shugaba Roch Marc Kabore dan shekaru 64 da haihuwa wanda yake kan madafun iko tun shekara ta 2015.

Tuni kungiyar ECOWAS/CEDEOA ta dakatar da kasashe biyu na Mali da Guinea Conakry daga ciki sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi.