1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: ECOWAS za ta hanzarta maido da zaman lafiya

September 15, 2020

Shugabanin kasashen kungiyar ECOWAS sun gudanar da taro na musamman inda suka tattauna rikicin siyasar Mali inda suka jaddada kudirinsu na ganin an mayar da kasar kan tafarkin dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/3iW4h
Mali politische Krise | Videokonferenz westafrikanische Führer
Hoto: Reuters/Ecowas

Shugaban kungiyar kana shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya ce a wannan rana ta Talata wa'adin da kungiyar ECOWAS ta debawa sojojin da suka yi juyin mulki a Mali na su samar da gwamnatin rikon kwarya ke cika, inda ya ce kungiyar ba za ta zuba idanu tana kalon kasar na ci gaba da tafiya ba tare da sahihiyar gwamnati ba.

To sai dai ga alama gwamnatin mulkin sojan Mali din bata amsa wannan kira na ECOWAS ba kasancewar ya zuwa yanzu ba ta fito da wani tsari na kafa gwamnatin ta rikon kwarya ba. 

Ya zuwa yanzu dai kungiyar ta ECOWAS ba ta ambata matakin da za ta dauka kan gwamnatin mulkin sojan Mali din ba, bayan karewar wa'adin da aka deba mata na girka gwamnatin rikon kwarya da za ta kunshi fararen hula.