Mutane hudu suka mutu a Senegal
March 7, 2021Talla
Kiran ya zo ne bayan kwashe kwanaki hudu ana bata kashi tsakanin magoya bayan jagoran adawar kasar Ousmane Sonko da jami'an yan sanda.
Fadan dai ya barke tun a ranar Larabar da ta gabata bayan kame jagoran adawar da jami'an tsaro suka yi wanda ya yi sanadiyar ajalin mutun hudu kawo yanzu.
ECOWAS din ta yi kira ga hukumomin Senegal da su dauki matakan da suka dace domin kawo karshen tashin tashinar.