SiyasaJamus
Juye-juyen mulki a yammacin Afirka sun mamaye taron ECOWAS
March 25, 2022Talla
Za a gudanar da taron a birnin Accara na kasar Ghana kuma ana sa ran shugabannin kasashen su kara daukar muhimman matakai ga sojojin da suka aiwatar da juyin mulki a kasashen Burkina Faso da Guinea Conakry, bayan dakatar da su daga jerin membobin kungiyar. Kana ana hasashen kungiyar ta shata wa sojojin da suka yi juyin mulkin wa'adin sake mika mulki a hannun wata gwamnatin farar hula.
Sai dai ana ganin batun jadawalin shirya zabe a Mali, zai kasance kan gaba daga cikin muhimman batutuwan da taron na ECOWAS zai mayar da hankali, musamman ma bayan da kungiyar ta kasa cimma matsaya da gwamnatin rikon kwarya a karkashin jagorancin Kanar Assimi Goïta kan batun wa'adin shirya zabe.