1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Ecowas ta ce a soke zaben da aka yi

July 27, 2020

Shugabannin kasashen yammacin Afirka na Ecowas sun bukaci da a soke zaben 'yan majalisu 31 da ya tada hankali da ma jefa Mali a cikin rudani, hakan ya biyo bayan taron da suka kammala.

https://p.dw.com/p/3g0CW
Mali Präsident Mahamadou IssoufouI aus Nigeria von Präsident Ibrahim Boubacar Keïta begrüßt
Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita tare da Shugaban kungiyar Ecowas Mahamadou IssoufouHoto: Présidence du Mali

A cikin kwanaki goma da ke tafe ne dai shugabannin kasashen Ecowas ke fatan suna iya kai wa ga matse ruwa daga dutse tare da sake dora kasar ta Mali a cikin zama na lafiya. Kuma sun kare wani taro na musamman kan Malin tare da daukar jeri na matakan da suke fatan na iya kwantar da hankula na gwamnatin kasar da kungiyar M5 da ke jayayya da gwamnatin kan mulkin kasar. Sanarwar bayan taron ta ambato cewar jerin matakan da kungiyar ta dauka sun hada da soke zaben 'yan majalisu 31 tare da sake sabon zabe, a wani abun da ke iya kai wa ga sanyaya zuciya ta kungiyar M5 din da ke fadin babu sahihanci a cikin zaben.

Ecowas ta umurci Shugaban Malin IBK da ya kafa gwamnatin hadin kan kasa

Krise in Mali | ECOWAS | Alassane Ouattara und Ibrahim Boubacar Keïta
Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara tare da Shugaban Mali IBKHoto: Présidence du Mali

Ecowas din dai ta kuma  nemi shugaban na Mali da ya kara kokari cikin neman ceton madugun adawar Malin Soumaila Cisse da aka sace a cikin watan Maris din da ya shude, da ya kasance a cikin muhimmai na dalilan tada hankalin. Ecowas din ba ta amince da  bukatar ta masu adawar da ke neman saukar shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ba daga shugabanci na kasar. Duk da cewar dai shugaba Keitan ya samu goyon baya na 'yan uwansa da ke Ecowas din, shugabanin sun kuma tilasta masa kafa gwamnatin hadin kan kasa da za ta kunshi daukaci na bangarori na kasar, a yayin da yake shirin nada firaminista da wasu jiga-jigan ministoci da suka hada da na tsaro, da shari'a da harkoki na waje da ma ministan kudin kasar.

Kungiyar Ecowas ta yi gargadin saka takunkumi ga dukkanin bangarorin da suka karya dokar sulhun

Krise in Mali | ECOWAS | Muhammadu Buhari und Boubou Cissé
Muhammadu Buhari tare da firaminista Mali Boubou CisseHoto: Présidence du Mali

Tun da farko dai shugaban tarrayar Najeriyar Muhammad Buhari ya ce kasar ta Mali na bukatar sassauci a daukaci na bangarorin biyu da nufin iya kai wa ga tabbatar da zama na lafiya a daukacin yankin Sahel. Wanda ya ce dole mu fahimci irin hatsarin da ke cikin yankinmu, hatsarin kuma da ke sassake a cikin batun rashin tsaro a yankin Sahel. Shugabannin Ecowas din dai sun ce suna shiri na kakaba takunkumi ga bangaren da ya sa kafa ya shure jeri na bukatun da ke zaman matakin karshe a kokari na sake dora Malin bisa ta farki na zaman lafiya.