1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS za ta zauna kan rikicin Burkina Faso

January 26, 2022

Kungiyar ECOWAS wacce ta ce ba ta ji dadin juyin mulki a Burkina Faso ba, za ta yi zaman tsara matakan da za su dace da halin da kasar ta samu kanta a ciki.

https://p.dw.com/p/468Ne
Nigeria | ECOWAS Gipfel
Hoto: Präsidentschaft von Niger

Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka wato ECOWAS, za su yi wani taro na musamman a ranar Juma'ar da ke tafe a kan kwace iko da sojoji suka yi a Burkina Faso da ma wasu kasashe na yankin.

A ranar Litinin da ta gabata ne sojoji a Burkina Fason, suka kifar da gwamnatin Shugaba Roch Marc Christian Kaboré, juyin mulki na uku ke nan a jere da yammacin na Afirka ke gani cikin tsukin watanni tara.

Gabanin kwace iko a Burkina Faso dai, sai da sojojin suka hambare gwamnati a Mali da ma na kasar Guinea Conakry.

Jagororin na kungiyar ECOWAS dai sun yi tir da kwace iko daga hannun Mr. Marc Kabore, suna mai cewa tilasta masa aka yi da ya yi murabus tare ma da yi masa barazana.

Juyin mulkin na Burkina Faso, ya zo ne yayin da kasar ke fama da hare-haren masu ikirarin jihadi da 'yan kasar suka bukaci tsohon shugaban da ya kawo karshen su.