1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

El-Baradei zai tattauna da jami´an Iran akan shirin nukiliyar ƙasar

January 11, 2008
https://p.dw.com/p/Co3b

Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta ƙasa da ƙasa wato IAEA a takaice ya isa birnin Teheran don yin shawarwari a dangane da wasu batutuwa da ba´a warware su game da shirin nukiliyar Iran. Mohammed El-Baradei yana kokarin shawo kan Iran da ta ba da cikakken haɗin kai wajen bayyana aikace aikacenta na nukiliya. Ana sa ran zai gana da manyan jami´an gwamnati ciki har da shugaba Mahmud Ahmedi-Nejad. Iran dai ta dage cewa shirin ta na sarrafa sinadarin uranium don amfanin farar hula ne kaɗai. To amma kasashen yamma na fargabar cewa tana iya amfanin da uranium din wajen kera makaman nukiliya, kamar yadda shugaban Amirka Georgfe W Bush ya kara jaddadawa a wannan mako yana mai cewa Iran barazana ce ga zaman lafiyar duniya baki ɗaya.