Embalo: Ba a rabu da Bukar kan juyin mulki ba
August 10, 2023Talla
Shugaba Umaro Sissaco Embalo ya bayyana haka ne a yayin ganawa da manema labarai a kan hanyarsa ta zuwa Abuja domin halartar taron kungiyar ECOWAS da zai gudana a wannan Alhamis.
Shugaban na Guinea Bissau wanda shi ma a baya ya fuskanci barazana ta yunkurin juyin mulki, ya kara da cewar har yanzu Shugaba Bazouum suka sani a matsayin halastaccen shugaban kasar jamhuriyar Nijar.
Embalo ya ce dole ne a haramta juyin mulki a yankin da ma kasashen Afirka baki daya, kuma duk wasu gungun mutane da ba sa son shugaba mai ci, to su bi hanyar dimokuradiyya wajen kawar da shi, ba wai ta juyin mulki ba.