Emmanuel Macron zai ziyarci Jamus
May 12, 2017Talla
A yayin ziyarar tasa dai, sabon shugaban Faransan Emmanuel Macron zai tattauna da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a da nufin yin nazarin hanyoyin kara kulla alaka tsakanin kasashen biyu akan sababbin tsare-tsarensu, game da makomar kungiyar Tarayyar Turai. Wannan dai na zama ziyara ta farko da sabon shugaban kasar ta Faransa zai yi zuwa wata kasar waje tun bayan zabensa a matsayin shugaba a Faransan, ziyarar kuma da ke zuwa kwana guda bayan ya yi rantsuwar kama aiki. Faransa da Jamus dai su ake kallo a matsayin kashin baya ga kungiyar ta Tarayyar Turai tun bayan kafa kungiyar a shekara ta 1957.