Erdogan ya gana da Rouhani kan ballewar Kurdawa
October 4, 2017Mahukuntan kasar Turkiyya sun ce sojoji hudu ne suka mutu a wani harin bam da ake zargin 'yan tawayen Kurdawa da kai wa a kudancin kasar. Akwai wasu sojoji hudu da suka samu rauni a harin na wannan Laraba. Wannan na zuwa ne a yayin da shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ke ziyara a kasar Iran, inda suka tattauna da takwaransa na Iran Hassan Rouhani kan illolin da ke tattare da yunkurin ballewar Kurdawa daga gwamnatin kasar Iraki da zummar samun 'yancin cin gashin kai a matsayin yankin Kurdawa zalla. Batun da ke haifar da fargabar ga makomar zaman lafiya a yankunan da ke ci gaba da fama da ayyukan mayakan kungiyar IS.
A baya gwamnatin Turkiyya ta dauki matakan soji na toshe kan iyakarta da yankunan Kurdawan a yunkurin nuna rashin goyon bayan zaben neman ballewar da ya gudana a makon jiya.