1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Falasdinawa na jimamin mutuwar Saeb Erekat

Mahmud Yaya Azare RGB
November 10, 2020

Falasdinawa da sauran kasashen Larabawa na ci gaba da jimamin mutuwar Saeb Erekat wanda ya sha gwagwarmaya a kokarinsa na son ganin an bai wa Falisdinawa 'yanci cin gashin kai.

https://p.dw.com/p/3l6aP
Palästina Saeb Erakat
Hoto: Issam Rimawi/AA/picture-alliance

Falasdinawa da shuwagabannin kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani kan rasuwar Saeb Erekat, babban na hannun daman Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, wanda kuma yake jagorantar tattaunawar da Falalsdinawan keyi da Isra'ila, bayan ya sha fama da jinya daga cutar corona, wacce daga bisani ta yi sanadiyar mutuwarsa.

Palästina Saeb Erakat
Erakat ya mutu bayan fama da cutar coronaHoto: Issam Rimawi/AA/picture-alliance

Saeb Erekat ya rasu yana da shekaru 65 a duniya, a cibiyar binciken lafiya ta Hadasa da ke birnin Qudus, birnin da ke karkashin mamayar Israila, shi ne babban na hannun daman marigayi Shugaban Falasdinawa Yaseer Arafat, dama Shugaban Falasdinawan mai ci Mahmud Abbas, yadda kusan shekaru 15 da suka gabata ya zama jagoran Falalsdinawa a tattaunawar da suke da Isra'ila a gwagwarmayar da Falalsdinawan keyi na ganin kafuwar kasarsu ta Falalsdinu ta tabbata.

Erekat ya mutu bayan kamuwa da corona yana da shekaru 65 a duniya

Isarel Netanya Saeb Erakat und Shimon Peres
​​​​​​Erakat da tsohon mataimakin Firaiministan Isra'ila marigayi Shimon PeresHoto: Ariel Schalit/AP Photo/picture-alliance

Erekat din da ke zama tsohon malamin Jami'a da yayi zurfi a kimiyar siyasa, da fari ana daukarsa mai sassaucin ra'ayin da yayi amanar cewa, hanyar tattaunawa da Isra'ila kan teburin shawara, ita ce hanya daya tilo da zata kai ga kafuwar kasar Falasdinu, kodayake daga baya ya rikide ya zama mai tsatstsauran ra'ayi, yadda ya dinga nuna adawa da tattaunawa da Isra'ila, sakamakon mamayar da take ci gaba da yi wa yankunan Falasdinawa ba kakkautawa. Gami da yankan bayan da Amirka ta yi wa Hukumar Falalsdinawa, yadda Amurkan da Isra' ilan suka hade baki,wajen hanawa hukumar ta Falalsdinawa kudaden gudanarwarta, kamar yadda yarjejeniyar kasa da kasa ta tanada.

Alhini kan mutuwar Erekat daga sassan duniya

Da dama daga cikin al'ummar Falalsdinawa dai nayi wa Erekat kallon dattijo kuma na kusa a hukumar Falalsdinawa da zai iya gadar Mahmud Abbas, lamarin da ya sanya suke daukar rasuwarsa tasa a matsayin babban rashi. Suma shuwagabannin duniya na ci gaba da turawa al'ummar Falalsdinawa da jagororinsu sakon ta'aziyya. Ofishin Mjalisar Dinkin Duniya da ke birnin Ramallah, a ta bakin kakakinsa, Mariyam Telcy ta sanar da cewa, duniya ta tafka asara da mutuwar wannan jarimin da ya jajirce kan bin matakan lumana da tattaunawa don kwatawa al'ummarsa hakkinsu. A yayin da ita ma kungiyar kasashen Larabawa a ta bakin kakakinta Yaseer Tilaimah ta ce, mutuwar Saeeb Erekat din babban rashi ne ga kasashen Larabawa dama Afirka da ma duniya baki daya.