1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erik Bettermann: "Jama'a ce manuniya ga ayyukanmu"

Johannes Hoffmann / Umaru AliyuMay 2, 2013

Ranar 3 ga watan Mayun shekarar 1953, tashar Deutsche Welle ta fara watsa shirye-shiryenta karo na farko. Shin tun daga wannan lokaci tsawon shekaru 60 ina matsayin tashar a yanzu?

https://p.dw.com/p/18Qcd
Intendant der Deutschen Welle
Hoto: DW

Daga wannan lokaci zuwa yanzu, wadanne al'amura ne suka canza, wadanne abubuwa ne har yanzu DW take rike da su? Wadannan suna daga cikin tambayoyin da shugaban tashar ta DW, Erik Bettermann ya amsa lokacin hira da aka yi da shi.

Bettermann dai yayi shekaru 12 a matsayin babban shugaban tashar ta DW. A wadannan shekaru da suka hada har da shiga canjin Millenium, wadanne al'amura ne suka dauki hankalin DW?

Shugaban gidan rediyon na DW ya amsa da cewar a fannin siyasa, babu shakka abin da yafi daukar hankali shine al'amuran da suka faru ranar 11 ga watan Satumba na shekara ta 2001 da duk abubuwan da suka biyo bayansu. 'Yan kwanaki kalilan kafin in karbi wannan mukami, na sami tabbas a game da muhimmancin DW ga kasarmu. Na ga muhimmancin samun muryar baiyana ra'ayi da ikon fadin albarkacin baki. Bayan wannan kuma babu shakka akwai ci gaban gaggawa da aka rika samu a bangaren fasaha. Wannan tsari ne da ya canza hanyoyin sadarwa a duniya baki daya. Hakan ya shafi samar da labarai, aiwatar da su da watsa su, tare da yadda masu kallo da sauraro suke daukarsu. Duka wadannan abubuwa ne da suka canza.

Shekaru takwas bayan kare yakin duniya na biyu, aka mika wa DW aikin fadakarwa da gyara sunan Jamus da share hanyar sake komawarta tsakanin sauran kasashen duniya. To yanzu, shekaru 60 bayan wannan lokaci wane aiki ya ragewa DW?

Erik Bettermann ya ce tun daga tushen kafa DW zuwa yanzu, aikinta shi ne ta nunar da darajar kasarmu ga sauran duniya. Aikin DW ta sanar wa duniya yadda Jamus ta zama kasa mai albarkar al'adu a nahiyar Turai, kuma kasa mai bin tsari da tafarkin demokradiyya. Wannan ma shi ne babban abin dake kunshe a tsarin dokokin DW na shekara ta 2005. Wadannan dokoki sun sabunta tsarin ayyuka da shirye-shiryen da muke gabatarwa sun kuma fadada su. Ta hanyar harsuna masu yawa da muke gabatar da shirye-shiryenmu na jarida, mun zama wani dandali na cudanyar al'adu, inda muke gabatar da bayanan al'amura yadda Jamus take kallonsu da yadda sauran kasashen duniya suke kallon wadannan al'amura. Saboda haka ne muke daukar kanmu a matsayin muryar 'yanci da kare hakkin 'yan Adam.

To shin me hakan yake nufi idan aka yi magana ta fuskar aikin jarida?

Burinmu shi ne mu kai ga masu sauraro a ko ina suke a duniya. Saboda haka ne muke gabatar da shirye-shiryenmu na jarida cikin harsuna 30. Tsarin dokokin aikin DW sune tushe dake jagorancin harsuna dabam dabam na tashar. Babban jagora ga aikinmu, shi ne neman cika bukatun masu sauraro da masu kallo da masu amfani da hanyar Internet. Da yake yankuna da nahiyoyin duniya sun banbanta, mukan yi iyakacin kokarinmu domin bai wa ko wane yanki bukatunsa. Hakan kuwa yana iya yiwuwa sakamakon ci gaban fasaha da aka samu da kuma canje-canje a fasahar masu hulda da mu. Hakan ma shi ya sanya shekara da shekaru muke amfani da fasahar gajeren zango domin watsa shirye-shiryenmu, muke kuma fadada shirye-shiryen Telbijin ta hanyar kumbunan satellite da bullo da shirin Internet, abin da a yau ya mai da mu masu gabatar da shirye-shirye ta hanyoyi da dama. Tun shekaru da dama muke watsa shirye-shiryen Telbijin ta amfani da tashoshi shidda zuwa yankuna dabam dabam, cikin harsunan Jamusanci, Ingilishi, Spaniyanci da kuma Larabci. Mukan kuma tsara rahotanni da karin bayanai cikin wasu harsunan, domin amfanin tashohin telbijin abokan huldodinmu. Shirin mu na Internet a yau kuwa, ya hada da hanyoyin sadarwa na zamani da na'urorin sadarwa na tafi-da-gidanka.

Ko da shike DW tana aiki ne karkashin tsarin da aka mika mata, sa'annan kudin tafiyar da wannan aiki yana samuwa ne daga hukuma, amma tashar ta yi shekaru 60 tare da cikakken 'yancin tafiyar da al'amuranta. A bisa lura da haka, ta yaya DW a wannan hali na tsaka-mai-wuya ta sami damar tabbatar da matsayinta na amintacciyar tasha ta watsa labarai?

A matsayinmu na tashar hukuma dake watsa shirye-shiryenta zuwa ketare, kuma mai samun kudaden tafiyar da ayyukan ta daga hukuma, muna da wata alfarma tsakanin sauran tashoshin dake watsa shirye-shiryensu zuwa ketare. Kamar dai sauran tashoshi na cikin gida, muna samun kariya daga fanni na biyar da kundin tsarin mulkin Jamus. Saboda haka ne ba'a samun matsala tsakanin aikinmu da kuma kasancewar hukuma ce take ba mu kudin tafiyar da aikin namu da cikakken 'yancin aikinmu na jarida. Sakamakon aikin jarida mai inganci da daidaituwar aikinmu na nunar da kasarmu yadda take a zahiri, tashar DW ta samar wa kanta suna a matsayin tasha mai inganci da gaskiya ta samun labarai da watsasu. Kari kan wannan kuma, mun kasance masu ba da murya ga duk wadanda ake take hakkinsu a kasashensu na asali. Masu sauraro sun amince da mu. Wannan kuwa shi ne daraja mafi girma duk wata tasha dake watsa shirye-shiryenta zuwa ketare za ta iya samu.

Shin wannan shi ne dalilin da ya sanya shirye-shiryen sashen horaswa na DW yake samun karbuwa mai yawa a duniya?

Yanzu dai kusan shekaru 50 kenan muna taimaka wa game da samar da tsarin aikin jarida mai cikakken 'yanci. Ma'aikatar taimakon raya kasashen ketare ta Jamus sannu a hankali tana zama abokiyar hadin kanmu mafi muhimmanci. Tun bayan shekara ta 1953, an sami canje-canje masu tsanani a duniya baki daya tare da tsarin yada labarai da hanyoyin sadarwa. Wannan ma shi ya sanya DW, ta tashi daga kasancewa tashar rediyo kadai, ta maida kanta tasha mai fannonin sadarwa iri dabam dabam, saboda duk tashar da ta kasa cimma bukatun kalubalen zamani, babu shakka za'a barta a baya. Tun da wuri muka dauki hanyar watsa shirye-shiryenmu ta amfani da fasahar digital. Mu ne kuma na farko daga cikin dukkanin tashoshin hukuma da ake da su a nan Jamus da muka fara yada shirye-shiryenmu ta Internet, mu ne kuma na farko da muka fara yada shirye-shiryen namu ta kafofi masu yawa, wato Rediyo da Telbijin da Internet. Duk wanda ya zo wurinmu domin samun horo, yakan sami kwarewa a fannoni da dama, tun daga aikin Telbijin har zuwa na Rediyo da Internet. Kafofin sadarwa na zamani kuwa, tuni suka zama na yau da kullum tsakanin dukkanin harsuna 30 da muke gabatar da shirye-shiryenmu da su.