Estoniya ta rungumi Euro
January 1, 2011Yau kasar Estoniya ta shiga sahun kasashe masu amfani da takardar kudin Euro. A Tallin babban birnin kasar an gudanar da kasaitacen buki na sallamar kudin Kroon da kasar ta yi amfani da shi gabanin haka. Gwamnatin kasar mai matsakaicin raayin gurguzu ta ce wannan sauyi zai samar ma kasar ci gaban tattalin arziki duk kuwa da matsalar da kudin na euro ke tsintar kansa a ciki a halin yanzu. Kasar ta Estotina dai na zaman kasa mafi talauci tsakanin kasashe masu amfani da kudin euro wadda jimilirar abin da take samu a gida bai zarta digo 8 daga cikin dari ba. A matsayin abin da ke zaman alamar wannan sauyi framinitan kasar, Andrus Ansip ya fid da takardar kudin Euro daga wani mashin na kudi a yayin bukin . Shugaban hukumar zartatarwar kungiyar Tarayyar Turai, Jose Manuel Boroso ya ce kenan yanzu yan kasahen turai sama da miliyan 330 ke amfani da kudin na Euro.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Eidita: Abdullahi Tanko Bala