A daidai lokacin da kasashen yankin Nilu ke kokarin kammala tattaunawa kan batun aikin gina Dam da Ethiopiya za ta yi a saman kogin, DW ta kai ziyarar gani da ido wajen aikin ginin Dam din wanda ya haifar da rikicin diplomasiyya tsakanin Habashar da Masar.