1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniKamaru

Eto'o na fuskantar turjiya daga alkalan wasa a Kamaru

Zakari Sadou MAB
January 4, 2024

Alkalan wasan kwallon kafa na Kamaru sun gudanar da zanga-zanga a Yaoundé saboda rashin samun albashin da suke bin Fecafoot. Amma Samuel Eto'o Fils da ke shugabantar hukumar ya dakatar da su har sai abin da hali ya yi.

https://p.dw.com/p/4araW
Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Kamaru Samuel Eto'o Fils
Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Kamaru Samuel Eto'o FilsHoto: Daniel Beloumou Olomo/AFP/Getty Images

Alkalan wasan kwallon kafa fiye da 100 ne suka fito zanga-zangar lumana a babban birnin Kamaru, domin nuna bacin ransu game da dakatar da su da aka yi da sunan sun shiga yajin aiki sakamakon rashin biyansu albashinsu da wasu bukatu na daban. Hasali ma dai, suna bin gwamnatin Kamaru da hukumar kwallon kafar kasar ta Fecafoot aikin alkalancin wasa da suka yi a kakar wasa ta 2022 zuwa 2023 da kuma na gasar cin kofin Kamaru na shekaru biyu da suka shude.

Karin bayani: Samuel Eto'o: Jagoran kwallon kafar Kamaru

Kwallon kafa ya fara sukurkucewa a Kamaru sabanin shekarun baya
Kwallon kafa ya fara sukurkucewa a Kamaru sabanin shekarun bayaHoto: DW/M. Kindzeka

Watanni da dama da suka shude, an samu zaman tattaunawa a tsakanin alkalan wasannin da kwamitin gudanarwar da wasan kwallon kafa na wucin gadi. Amma  zaman bai haifar da wani ci-gaba ba. Duk kokarin tuntubar mambobin Fecafoot da DW ta yi domin samun karin haske ya ci tura. Su dai alkalan na bukatar kulawa ta musamman saboda a wani lokaci sun sadaukar da wani bangare na rayuwarsu domin bayar da gudunmawa a harkar kwallon kafar Kamaru.

Achtelfinale Ägypten Kamerun Afrik Cup
Lokacin da Achille Emana ya ci kwallo a gasar Afcon a gaban Masar a 2010Hoto: AP

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan wasan kwallon kafa na babban liga na Kamaru suka dakatar da buga wa kungiyoyinsu kwallo sakamakon rashin biyansu albashi da alawus-alawus.Isma'ila Mohaman, masanin wasan kwallon kafa ya danganta tsarin tafiyar da hukumar wasan kwallon kafa da Eto'o ke yi da tsarin kama-karya.

Ya ce: "A gaskiya Samuel Eto'o Fils ya ba mu kunya, kuma muna takaicin mara masa baya a zabensa da aka yi. Mun yi tsammanin zuwansa zai canza alkiblar kwallon kafa, amma a gaskiya ya kawo mana wani sabon tsari na kama-karya wanda a halin yanzu ba zai haifar da ci-gaba ba."

 Alkalan wasan na Kamaru sun yi barazana shiga yajin cin abinci muddin ba a magance matsalolin da suke fuskanta ba.