EU: Alakanta Rasha da Ta'addanci
November 23, 2022Talla
Majalisar dokokin kungiyar Tarayyar Turai ta ce, dakarun Moscow na kai hare-hare kan fararen hula da cibiyoyin makamashi da makarantu da kuma asibitoci, wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Hakan na zuwa ne bayan da 'yan majalisar suka kada kuri'ar amincewa da ayyana Rashar a matsayin kasar da ke daukar nauyin ayyukan ta'addanci, baya ga tarin takunkumai da kungiyar ta kakaba Rasha a baya sakamakon mamayar da ta kaddamar a Ukraine.
Dama da shugaba Volodymyr Zelenskyy ya bukaci Amirka da sauran kasashe kan su amince da Rasha a matsayin kasar da ke aikata ta'addanci. Har yanzu dai sakataren harkokin wajen Amirka Antonya Blinken ya ki amincewa da ayyana Rashar, duk da kudurin da aka cimma a majalisun wanda suka bukaci ya yi hakan.