EU na binciken aikata laifin cin hanci da rashuuwa
December 11, 2022Talla
Alkali mai shigar da kara a Beljiyam na tuhumar matar 'yar Girka Eva Kaili, da karbar cin hanci daga Qatar, wacce ke karbar bakwancin gasar cin kofin duniya a yanzu haka, kana da amfani da matar don samun goyon bayan majalisar dokokin nahiyar Turai ta hanyar biyan wasu kudade kai tsaye ko kuma ba da na goro.
Mme Kaili na daga cikin mutane biyar da hukumomin Beljiyam suka cabke a wannan Jumma'a, bayan da suka kaddamar da bincike, to amma za ta ci gaba da karba sunan mukaminta har sai bayan majalisar dokokin ta EU ta kada kuri'ar tsigeta daga mukamin.