1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaVenezuela

Venezuela: Kalubale ga Nicolas Maduro

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 10, 2025

Babbar jami'ar hulda da kasashen ketare ta kungiyar Tarayyar Turai EU Kaja Kallas ta ce, EU za ta ci gaba da aiki da dukkan al'ummar Venezuelan domin tabbatar da samun mafita ta dimukuradiyya a kasar.

https://p.dw.com/p/4p2UC
Venezuela | 2025 | Shugaban Kasa | Venezuela
Shugaba Nicolas Maduro ya yi rantsuwar kama aiki a karo na uku a VenezuelaHoto: Jhonn Zerpa/Miraflores Palace/Handout/REUTERS

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro da ya sake shan rantsuwar kama aiki a karo na uku a Venezuela, na fuskantar kalubale bayan da 'yan adawa suka bayyana cewa mai shekaru 62 a duniyar ya yi magudi tare damurde zaben shugaban kasar da aka gudanar a bara. Haka nan ma Amurka da wasu kasashen Latin Amurkan da dama, sun bayyana amincewarsu ne da jagoran adawa Edmundo Gonzalez Urrutia a matsyin halastaccen zababben shugaban kasa a Venezuela.