Barazanar rufe Twitter a Turai
December 1, 2022Talla
Kungiyar EU ta gargadi sabon shugaban Twitter Elon Musk kan bukatar kara tsauraran matakan yaki da kalaman batanci da cin zarafin al'umma da kuma yada labaran karya a kafar sadarwar.
EU ta ce saba sabbin dokokinsu ka iya kai su ga cin sa tarar makudan kudi ko ma haramta shafin gabaki daya a kasashen nahiyar.
Kwamishinan kungiyar a kan manufofin yanar gizo ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da suka yi a jiya Laraba. Sai dai kamfanin na Twitter ya sha alwashin bin ka'ida kamar yadda suka saba.
A farkon shekara mai kamawa ne manyan kamfanoni intanet za su fara amfani da sabbin dokokin da kungiyar ta EU ta samar .