Shugabar EU ta soki matakin Turkiyya
March 2, 2020Talla
von der Leyen ta fadi haka ne a yayin da take kalaman tausayawa Turkiyya kan halin da sojojinta ke ciki a yankin Idlib na kasar Siriya. Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai na shirin kai ziyara iyakar kasar Girka da Turkiyya, domin daukar matakin kwarar bakin haure.
Girka ta dakatar da shirin ba da mafaka saboda katse dubban 'yan gudun hijira da ke tsallakawa iyakarta daga Turkiyya, bayan da Shugaba Raccep Tayyip Erdogan, ya dauki matakin bude iyakar domin neman goyon bayan kasahsen kan rikicin Siriya.