EU: Bukatar hana shawagin jiragen sama a arewacin Siriya
March 5, 2020Ministocin harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai EU sun gudanar da taro a wannan Alhami din a Zagreb domin tattauna halin da ake ciki musamman batun 'yan gudun hijira a kan iyaka tsakanin Turkiyya da kasar Girka da kuma yanayin da lardin Idlib na Siriya yake ciki.
Ministan harkokin wajen Croatia Gordan Grlic Radman da babban jami'in harkokin wajen tarayyar Turai Joseph Borrel suka karbi bakuncin taron.
A yayin tattaunawar Borrel ya baiyana goyon baya ga bukatar Turkiyya na shata wata da'ira ta hana shawagin jiragen sama a arewa maso yammacin Siriya.
Sai dai yace ya rage ga kungiyoyi kamar NATO da Majalisar Dinkin Duniya su shata da'irar hana shawagin jiragen saman.
A waje guda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kiran samar da wani yanki na tsaro domin kare fararen hula.