1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin agajin soji ga kasar Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
October 17, 2022

Ministocin harkokin kasashen ketare na kungiyar tarayyar Turai za su yi wata ganawa a kasar Luxembourg da zummar amincewa da samar da horo ga dakarun kasar Ukraine da ma yiwuwar samar da karin agaji na kudi.

https://p.dw.com/p/4IGci
Prag | EU Außenminister
Hoto: Majda Slamova/European Council

A makon da ya gabata ne jakadun kasashen kungiyar ta EU suka bukaci a samar da wani sansani na musamman da zai horas da sojojin na Ukraine, wanda a yau ministocin za su amince da shi a hukumance.

Sama da yuro miliyan dari hudu ne ake shirin kara wa Ukraine, wanda ya kai adadin tallafin da kasar ta samu tun farkon mamyar da Rasha ta kaddamar mata ya zuwa sama da biliyan 3 na yuro ga bangaren ayyukan sojinsu kadai.

Babban jami'in harkokin kasashen ketare na Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya bukaci karin tallafi na makamai ga Ukraine, kasar da ta kwashe sama da wataani 8 ta na fama da yaki da Rasha.