1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Kayayyaki sun yi tsada saboda yakin Ukraine

Abdullahi Tanko Bala
July 14, 2022

Hukumar tarayyar Turai ta yi hasashen tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki a nahiyar Turai sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa kasar Ukraine wanda ya janyo tsadar abinci da makamashi.

https://p.dw.com/p/4E9fb
Bildgalerie 50 Jahre Römische Verträge I Symbolfoto Eurokrise
Hoto: Christoph Hardt/Geisler-Fotopress/picture alliance

Hukumar tarayyar Turai ta ce tana hasashen mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine zai kara tashin farashin kayayyaki zuwa kashi 7.6 cikin dari wanda aka dade ba a gani ba. Bugu da kari hukumar ta kuma yi hasashen za a sami tsaiko a cigaban tattalin arziki a 2022 da kuma 2023.
 
Tsadar kayayyaki a kasashe masu amfani da kudin euro ya yi matukar tashi saboda yakin Ukraine kamar yadda hukumar tarayyar Turan ta wallafa.

Mataimakin shugaban hukumar Turan Valdis Dombrovskis ya ce yakin Rasha a kan Ukraine na cigaba da dakushe hasken tattalin arziki a nahiyar Turai.

Yakin dai ya haifar da tashin gwauron zabi na farashin abinci da makamashi a Turai yayin da kasashe ke fafutukar lalubo hanyoyin da za su kauce wa takunkumin da aka sanya wa wasu muhimman kayayyaki.