Shugabannin kungiyar EU na neman mafita
July 2, 2019Talla
Duk da kai ruwa rana kan rashin fahimtar juna tsakanin jiga-jigan kungiyar tsawon kwanaki ana gudanar da taro, amma Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana fatan cimma matsaya tare da nada kusoshin kungiyar a zaman da shugabannin kungiyar za su yi karo na uku.
Ana adai ganin jinkirin samar da sabbin shugubannin kungiyar cikin lokaci ka iya zama matsala da zai rage tasiri da kimar kungiyar da ma tsarin makomarta nan gaba.