1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na shirin daukan sabon mataki kan Rasha

August 30, 2014

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai, za su duba batun tsaurara takunkumai ga kasar Rasha, wadda ake zargi da tura sojoji a gabacin kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/1D44y
Hoto: picture-alliance/dpa

Dayake magana yayin wata tattaunawa da shugaban Urkraie Pero Porochenko a birnin Brussels, Shugaban kwamitin Tarayyar Turai José Manuel Barroso 'yan sa'o'i kalilan kafin babban taron gaggawa na Tarayyar Turai kan batun rikicin kasar ta Ukraine, ya ce suna cikin wani yanayi mai sarkakiya, inda ya kara da cewa muddin rikicin ya ci gaba da karuwa gabacin na Ukraine, to suna iya kai wa ga matsayin da ba za a iya ja da baya ba.

Daga nashi bengare Shugaban kasar Ukraine Petro Porochenko, cewa ya yi mu zaman lafiya muke so ba yaki ba, amma kuma muna daf da bakin iyakar da idan muka fada babu ja da baya, inda ya zargi kasar Rasha da laifin tura sojoji da ma tankokin yaki a gabacin kasar ta Ukraine. Daga nashi bengare shugaban kasar Faransa François Hollande da ke jagorantar taron shugabannin gwamanatocin Socialiste na Tarayyar Turai, ya ce babu tantama sai an karawa Rasha takunkumi dangane da rikicin kasar ta Ukraine.

Mawallafi: Saliaaou Boukari
Edita : Suleiman Babayo