1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na son sabon shiri da Turkiyya kan bakin haure

Abdul-raheem Hassan
June 21, 2021

Ministan Harkokin waje na kasar Jamus Heiko Maas na neman kulla sabuwar yarjejeniya tsakanin kasashe mambobin EU da kasar Turkiyya kan miliyoyin 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/3vGSE
Heiko Maas Pressekonferenz Berlin
Hoto: AXEL SCHMIDT/REUTERS

Kungiyar tarayyar Turai EU tana da matukar sha'awar samun hadin kai na cigaba da gwamnatin Ankara wajen samar da yarjejeniyar kula da bakin haure.

Da yake ganawa da jaridar "Welt" Maas ya fada cewa duk da matsalolin da ke akwai tsakanin EU da Ankara, amma wajibi a yaba mata kan daukar nauyin kula da 'yan gudun hijira akalla miliyan hudu.

Ministan harkokin wajen na Jamaus wanda dan jam'iyyar SPD ne, ya nuna bukata ta musamman daga bangaren kasashe mambobin EU na samar wa Turkiyya karin kudaden gudanarwa a matasyin tagomashi na sabuwar yarjejeniyar.