1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na son sai ta kara wa Rasha takunkumi

May 29, 2022

Bayan samun wani tsaiko a kwanakin baya, kasashen Tarayyar Turai sun sake wani taron neman tabbatar wa Rasha karin takunkumi saboda mamayar da ta kai wa Ukraine.

https://p.dw.com/p/4C0zp
Ursula von der Leyen I REPowerEU
Hoto: Valeria Mongelli/ZUMA/IMAGO

Jakadun kasashen Tarayyar Turai 27, sun yi wani zama na nemo hanyoyin warware wani tarnaki da suka samu a game da aniyarsu ta kara takunkumin karya tattalin arzikin Rasha karo na shida, mai alaka da dakatar da shigo da mai daga Moscow.

Tun da fari dai kasar Hungary ce ta toshe shirin kasashen na EU, kasar da ke da karfi ta fuskar zirga-zirgar jiragen da ke dakon man daga Rasha.

Faransa wacce ke shugabancin kungiyar EU a yanzu, ita ce ta gabatar da bukatar sake duba batun a wannan Lahadin ta yadda za su ci gaba da ganin sun ladabtar da Rasha saboda wutar yaki da  kunna a Ukraine.

Kasar ta Hungary dai na dogaro ne da danyen man kasar Rasha da akalla kashi 65%, wanda ake aikawa ta bututun nan na Druzhba wanda ya fi kowanne girma a duniya.