EU na yaƙi da ta'addanci a Sahel
August 3, 2012Tawagar ƙwarrarun wacce za ta kasance a ƙarƙashin jagoranci shugaban hukumar rundunar tsaro ta fari kaya na ƙasar Spain kanal Francisco Espinosa ta fara aiki ne a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar tun ranar ɗaya ga wata Augusta tare da wakilai guda 50:
Babban aiki da ke a gaban wannan tawaga da aka yiwa la'aƙabi da suna da sunnan EU-Sahel-ko kuma EUCAP na da zumar ƙara ba da horo na jami'an ƙungiyar Tarrayar Turai ga ƙasashen yankin sahel domin yaƙi da ta'addanci
Michael Mann shi ne mai magana da yawun ƙungiyar ta Tarrayar Turai ''ya ce tawaga ce ta jami'an na farin kaya, ya ce amma wasu na aza ayar tambaya inda aka ce da su ƙwarraru ne ta fuskar aikin soji , ya ce alllah kuli hali idan ana son yaƙi da ta'addanci tilas ne a yi kira ga masu ƙore wa ta fannin illimi aikin soji, amma ba wai ina nufi cewar za mu tura sojoji ne ɗauke da makamai ba.
Nijar ta buƙaci EU ta taimakama ta domin murƙushe yan ta'adda na Aqmi da Al-Qaida
Babbu shakKa zuwan wannan tawaga ya na da nasa ba ne da abinda ke faruwa na ta'adanci a cikin ƙasashen yankin Sahel inda masu kishin islama suka yi sansani musamunma a arewacikin ƙasar Mali wanda kuma suke da alƙa da ƙungiyar AL-Qaida dakuma Aqmi.Tilas ne a cikin irin wannan yanayi aikin kiyaye tsaro ta hanyar samun baiyana siri ga yan sanda da kuma sojoji ya zama kan gaba wajan yaƙar yan ta'addar.
Kusan za a iya cewar yankin yammancin Afirka kama daga Aljeriya Moritaniya har zuwa Nijar ,yankunan da ke fuskantar barazana; kakakin ya ci gaba da cear dalilan da suka sa ne ma kennan kasar Nijar tuntuɓe mu.''ya ce hukumomin Nijar su suka buƙaci mu taimaka masu ta fuskar ba da horo ga jami'an tsaron su domin samun ƙore wa da za ta basu damar yaƙi da ta'adanci domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar da ma yakin yamman Afirkan baki ɗaya.
EU na da niyar aiwatar da irin wannan shiri na ba da horo a gaba ga jami'an ƙasashen Mali, da Moritaniya
Wannan shiri na ƙungiyar ta Tarrayar Turai zai ɗauki tsawon shekaru biyu a Nijar kuma a shekara ta farko za a kashe kudi kamar Euro bilayan takwas hada rabi sannan a cikin shekaru masu zuwa a kwai watakila yiwar a faɗaɗa shirin zuwa ƙasahen Mali da Moritaniya dukani su masu fama da rashin tsaro.Amelia Hadfiel ƙwarrara ce akan yankin Sahel kana kuma malama a jami'a Vrije da ke a birnin Brussel na kasar Beljium.''ta ce masamun ma yadda ƙasahen Moritaniya da Mali da Nijar ke da rauni ta fuskar tsaro saboda rashin hali na wahalolin da ke a gaban su inda komai yayi ƙaranci akan abinda ya shafi ruwan sha; da wutar lantarki, da illimi da kuma kiwon lafiya, idan aka taimaka masu zai rage wasu larurorin .
Du dama cewar ƙungiyar Tarrayar Turai ta yi ɗamarar' yaƙi da ta'adanci akan manufofin da ta sama gaba amma kuma suna yi suna dubin bakin gatari domin suna gani aiwatar da hukumci ta fuskar yin shara'a mai adalci ga masu aikata laifufukan ta'addanci shi ne abinda za a fi mayar da hankali akai ,ba wai kawai ba, a yi ta yin farautar su.
Mawallafi:Abdourahamane Hassane
Eita : Abdullahi Tanko Bala
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto