1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta farfado da tattalin arzikinta

July 8, 2020

Hukumar gudanarwar Tarayyar Turai ta amince da shirin Jamus na tallafa wa tattalin arzikin kasar da ya fuskanci koma-baya sakamakon annobar Covid-19.

https://p.dw.com/p/3eyai
Belgien EU-Parlament Angela Merkel
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Seco

A wani yunkuri na ragewa masana'antu radadin halin da suka shiga sakamakon bullar annobar Corona, hukumar gudanarwar Tarayar Turai ta amince a hukumance da shirin gwamnatin Jamus na ba da tallafin Euro miliyan dubu biyar domin farfadowa da tattalin arzikin kasar.

Matakin da hukumar ta dauka na zuwa ne a daidai lokacin da kasashe mambobin kungiyar ke ta da jijiyoyin wuya kan wadanda za su amfana da agajin. Tsarin dai zai mai da hankali ne a kan kamfanonin da annobar ta shafa kai tsaye, ban da wadanda suka shiga rudanin kudade kamin bullar annobar ta Covid-19.

Wannan tsarin shi ne za a ci gaba da aiki da shi har karshen wannan shekarar ta 2020.

Hukumar Tarayyar ta Turan ta ce  za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da sauran mambobin kungiyar ta yadda za a ceto masana'antun kasashen.