EU ta bai wa Rasha wa'adin kwanaki uku
June 27, 2014Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai dake gudanar da zaman taron su na kwanaki biyu, a birnin Brussels, sun baiwa kasar Rasha wa'adin kwanaki uku, domin tayi duk abun da ya dace, na ganin an samu sassauci a rikicin gabacin kasar Ukraine, muddin kuma ba haka ba, zata fuskanci karin sabin takunkumi.
Kungiyar ta EU dai, ta gindaya sharudda har guda 4, da ta kamata a shayo kansu kafin ranar Litinin (30.06.2014), cikin su kuwa har da batun ci-gaba da tataunawa, bisa amfani da tsarin zaman lafiyar da Shugaba Petro Porochenko na Ukraine ya fitar.
Daga nashi bengare, Shugaban kasar ta Ukraine, ya kara wa'adin tsagaita wuta na kwanaki uku, a rikicin da gabacin kasar ke fuskanta tsakanin dakarun gwamnatin kasar da 'yan aware masu goyon bayan Rasha.
Shugaba Porochenko, ya dauki wannan aniya ce, dan bada dama, kan tataunawar da ake ta neman sakin 'yan kungiyar nan ta tsaro da hadin kan Turai ta OSCE, da batun samun sa'ido kan iyakokin Rasha da Ukraine.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe