EU ta bukaci tsawaita takunkumi kan Rasha
May 26, 2017Talla
Tusk ya bayyana wannan mataki ne a yayin da shugabannin kasashe mafi karfin tattalin ariki a duniya ke ganawa a yankin Sicilya na kasar Italiya. To sai dai Amirka bata fito karara ta bayyana matakinta kan wannan yunkuri ba.
A shekarun bayane kungiyar tarayyar Turai da gwamnatin tsohon shugaban Amirka Barack Obama, suka kakabawa Rasha takunkumi kan yadda ta mamaye yankin Kirimiya dama iza wutar rikici tsakanin dakarun gwamnati da masu adawa a gabashin Ukraine.
To sai dai babu tabbacin ko sabon shugaban na Amirka Donald Trump zai mutunta takunkumin ko a a, ganin yadda yake fama da Rasha akan zargin kutsen yanar gizo a lokacin zaben kasar a bara.