EU ta caccaki Trump kan yarjejeniyar Iran
October 16, 2017Talla
Kasashe mambobi kungiyar EU, sun soki matakan shugaban Amirka Donald Trump da ke neman dakile yarjejeniyar Nukilyar Iran. A yayin wata ganawa mambobin kungiyar a Luxemburg, EU ta ce wadannan matakan ka iya haifar da tabargaza a yunkurin sulhunta wutar rikici da ke ruruwa tsakanin Koriya ta Arewa da sauran kasashen duniya kan sarrasa makaman kare dangi.
Babbar jami'ar harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini ta ce "Ina sa ran dukkanin mambobin kungiyar EU, za su ci gaba da mutunta yarjejeniyar ci gaba da kulla dangantaka da kasar Iran. Kada a sake a ba da fuska da yunkurin Trump, wanda ka iya rusa shirin shiga tsakani da gwamnatin Pyongyang."