EU ta yi tir da matakin rufe ofishin DW a Moacow
February 4, 2022Talla
Da yake jawabi ga manema labaru, mai magana da yawun Kungiyar ta EU a kan harkokin kasashen ketare, Peter Stano ya ce wannan mataki ne da ba za su amince da shi ba, ya kuma ce Rasha ta nuna yadda ta ke ci gaba da murkushe 'yancin yada ayyukan jarida.
Wannan matakin da Rasha ta dauka dai na zuwa ne bayan da Jamus ta haramta watsa wasun shirye-shirye cikin harshen Jamusanci a tashar Russia Today wanda kuma Stano ya ce ko kusa ba su da alaka da abin da Rashar ta yi.
EU ta ce tana goyon bayan tasahar DW da ma ma'aikatan da abin ya shafa. Wannan sabuwar ta'akadamar ta kara rura wutar rikici da dama can ke ci tsakanin mahukuntan na Moscow da EU a game da yunkurin mamaye wani yanki na Ukraine.