1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta ce tana tare da masu neman mafaka

Yusuf BalaAugust 31, 2015

Hedikwatar EU da ke a Brussels za ta kara bada miliyan biyar na Euro dan tallafa wa kasar ta Faransa cikin ayyukan jinkai da take yi na taimakon 'yan gudun hijira dubbai da ke a yankin na Calais.

https://p.dw.com/p/1GOUH
Frankreich Manuel Valls in Calais mit Timmermans und Avramopoulos
Manuel Vallsministan harkokin cikin gidan Faransa a yankin Calais da Timmermans na EU da sauran jami'aiHoto: Getty Images/AFP/D. Charlet

Mataimakin shugaban hukumar Tarayyar Turai, Frans Timmermans ya bayyana cewa ba zasu taba juya baya ba ga duk wadanda ke neman tsira da rayukansu.

Timmermans ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara a gabar teku da ke Arewacin Faransa a yankin Calais a ranar Litinin din nan.

Ya kara da cewa hukumar tasu da ke da hedikwata a Brussels za ta kara bada miliyan biyar na Euro dan tallafa wa kasar ta Faransa cikin ayyukan jinkai da take yi dan taimakon 'yan gudun hijira dubbai da ke a yankin na Calais a bisa muradinsu na danganawa da kasar Birtaniya.Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta ce babu batun tsaurara dokoki a lamuran da suka shafi 'yan gudun hijira.