Syriya na daya daga cikin matsalolin yan gudun hijira
September 25, 2015Talla
An bayyana cewar Tarayyar Turai na iya ci gaba da fuskantar kwararowar 'yan gudun hijira ko da kuwa kasashen duniya sun sami nasarar kawo karshen rikicin siyasar kasar Syriya.Bayanan hakan sun futo ne daga bakin shugaban harkokin manufofin kungiyar EU Federia Mogherini a ranar jumma’ar nan bayan wata ganawa da ya yi da manema labarai.
Mogherini ya ce kasar Syriya ita ce da ke da dumbun masu gudun hijira da ke a warwatse a tarayyar Turai, a don haka bai kamata mu yaudari kan muba domin Syriya nada yan gudun hijira miliyan hudu tare da karin miliyan takwas da ke warwatse a yankin larabawa a kawai kuma Karin wasu matsalolin da suka hada da yake-yake da yunwa a ta cewar Federicia Mogherini.