EU za ta rage amfani da makamashin Gas
July 26, 2022Talla
Babban kamfanin makamashin gas na Rasha Gazprom ya sanar da cewa daga wannan Larabar zai rage yawan makamashin da yake sayar wa kasashen Turai, lamarin da ke barazana ga kasashe kamar Jamus wadda ta dogara sosai akan Moscow wajen samun makamashin da ta ke amfani da shi a masana'antunta.
Kasashe 27 mambobin kungiyar tarayyar Turai EU wadanda suka sanya wa Rasha takunkumin tattalin arziki domin hukunta ta saboda mamayar da ta yi wa Ukraine, sun amince da matakin rage amfani da gas din da kuma raba nauyin karancin makamashin a tsakaninsu.
Matakin dai na daga cikin dabarun da za su dauka na yin tsimin makamashi gabanin lokacin sanyin hunturu idan Rasha ta katse samar musu da makamashin na gas.