EU ta cimma matsaya kan tsadar makamashi
October 21, 2022Talla
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin taron kolin kungiyar na kwanaki biyu da ke gudana a birnin Bruseels na kasar Beljiyan domin lalubo hanyoyin magance matsalar makamashi da nahiyar ke fuskanta.
Har kawo safiyar wannan Juma'ar, an gaza dinke barakar da ke tsakanin wasu kasashe, wajen cimma matsaya kan kayyade farashin iskar gas. Sai dai shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce taron ya samar da tubali da zai bada damar ci gaba da aiki kan farashin makamashin.
A kalla kasashe 15 ne daga cikin 27 na mambobin kungiyar, suka amince da kayayyade farashin iskar gas don sassauta tsadar rayuwa da ake fama da ita. Sai dai Jamus da Faransa sun nuna adawa da wannan matakin, amma daga baya Jamus ta janye matsayinta.