1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai ta kayyade

Ramatu Garba Baba
December 19, 2022

Ministocin Kungiyar tarayyar Turai sun cimma matsayar kayyade farashin makamashin gas bayan shata wasu sabbin sharudda a zaman da suka yi a birnin Brussel.

https://p.dw.com/p/4LCL7
Hoto: Olivier Matthys/AP Photo/picture alliance

Bayan an jima ana kai ruwa rana, a wannan Litinin kasashe mambobi a tarayyar Turai suka cimma matsaya kan kayyade farashin makamashin gas bayan shata wasu sharudda. Tun a watan Augusta da farashin gas din ya tashi, akasarin kasashen na Turai suka soma yunkurin shawo kan al'amarin ta hanyar daidaita farashin amma suka fuskanci turjiya daga wasu mambobinta kamar Faransa da Jamus da suka nuna rashin gamsuwa da wasu daga cikin sharuddan da suke ganin sun yi tsauri.

A martanin da ta mayar bayan sanar da kayyade farashin a hukumance, Rasha ta ce, al'amari ne da ba za ta lamunta ba, daman a can baya, ta riga ta yi barazanar kin sayar wa duk kasar da ta bi tsarin na EU.