EU ta dauki mataki kan tauye hayakin motoci
December 8, 2016Talla
Kungiyar tarayyar Turai ta fara daukar matakin shari'a a kan Jamus da Birtaniya da kuma wasu kasashe biyar mambobinta dangane da gazawar su wajen sa ido kan almundahana a gwajin hayaki na wasu kamfanonin motoci, bayan tabargazar kwange da kamfanin Volkswagen ya yi na hayaki a motocinsa masu amfani da man diesel.
Jami'ai a kungiyar ta EU suka ce kungiyar ta damu matuka cewa, gwamnatoci na hada baki da manyan kamfanonin motoci wajen tauye gaskiyar bayanai game da gurbataccen hayaki da motocin ke fitarwa wanda kuma ke da illa ga lafiyar bil Adama.
Ana dai zargin kasashen Jamus da Birtaniya da Spain da kuma Luxemburg da rashin daukar tsauraran matakai kamar yadda kamfanin kera motocin Volkswagen ya fuskanta a Amirka.