1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta fara aiki da takunkumin man fetur kan Iran

Umaru AliyuJuly 2, 2012

Kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai sun dakatar da cinikin man fetur da Iran domin matsawa kasar lamba kan nukiliya

https://p.dw.com/p/15Pwf
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan takunkumi na Turai ya sanya tilas kenan kungiyar ta daina samun man fetur daga Iran yayin da mahukunta a Teheran tilas su daina samun kudi daga kugiyar ta hadin kan Turai, ko da shike bangarorin biyu, duk da irin gaba da kyamar juna dake tsakanin su, amma suna bukatar junan su. Ya zuwa wnai dogon lokaci, kasar da ita ce ta hudu a jerin wadanda suka fi samarda man fetur a duniya da kuma nahiyar da ita ce ta biyu da tafi amfani da man fetur a duniya zai zama wajibi ne hada kai, saboda suna bukatarf juna. Ana iya duba alkaluma a zahiri, a ga bangaren da takunkumin zai fi yiwa illa.

Misalin kashi daya cikin kashi biyar na man fetur da Iran take sayarwa a ketare ana kawo shi kungiyar hadin kan Turai ne, inda Jamus take sayen kashi daya cikin dari na man fetur da take bukata daga kasar ta Iran. A daya hannun kakakin kungiyar hadinkan Turai, Michael Mann yake cewa:

Idan aka yanke man fetur da Iran take sayarwa a kasashen kungiyar hadin kan Turai, za'a yanke babban abin da kasar take samun kudin ta daga gareshi kenan. Amirka ta dauki irin wannan mataki, saboda haka Iran din zata kasance cikin mummunan hali na matsin lamba, abin da ake fatan zai tilaswa gwamnatin ta Iran ta koma kan teburin shawarwari, ta kuma tattauna yadda ya kamata.

A nan nahiyar Turai kuwa, Girka ita ce kasar da zata fi fama da matsala, kamar yadda masani kan harkokin man fetur, Volker Blandow, daga cibiyar nazarin al'amuran man fetur dake birnin Munich ya nunar. Girka din tana da yarjejeniya tsakanin ta da Iran, wadda a karkashin ta, bai zama tilas kasar ta biya kudin man fetur da Iran take bata nan take ba. To amma yanzu, inji Blandow, sakamakon takunkumin na Turai, tilas Girka ta nemi man da take bukata daga kasuwannin hada-hadar man fetur, wanda kamar yadda aka sani, Girka din bata da kudin yin hakan a yanzu. A daya hannun, Spain da Italiya, sauran kasashe biyu da suka fi sayen mai daga Iran, tuni sun canza sheka, inda zasu rika samun man da suke bukata daga Saudi Arabiya.

Iran Atom Atomverhandlungen Moskau
Shawarwari kan shirin atom na IranHoto: Fars

Kasar Iran ma wannan takunkumi zai haifar mata da mummunan illa, kamar yadda masana da dama, cikin su har da Volker Blandow suka yi hasashe.

Tun daga ranar daya ga watan Yuli, kungiyar hadin kan Turai ta daina sayo danyen man fetur daga kasar Iran. Kungiyar tayi hakan ne domin matsa lamba ga Iran tayi sassauci ga manufofin ta. Kasashen kungiyar sun nuna cewar ba zasu sake kyale jiragen ruwan daukar man fetur daga Iran su isa tashoshin su ba, sai Iran tayi alkawarin zata shiga shawarwari sosai game da shirin ta na atom. Kungiyar hadin kan Turai da Amirka suna zargin Iran din ne da laifin amfani da wannan shiri domin kerawa kanta makaman nuclear. Ita kanta Iran ta musunta haka, inda tace tana da yancin amfani da fasahar atom domin samun makamashi.

Tattalin arzikin Iran ya dogara ne sosai kan kudin da kasar take samu daga cimnikin man fetur dinta a ketare. Har m,a ana cewar man fetur din shine ke samarwa kasar tsakanin kashi 30 zuwa kashi 40 cikin dari na kudaden da take samu gaba daya. Idan kuma daga wannan adadi aka yanke kashi 20 ko kashi talatin cikin dari, kasar zata ji zafin hakan matuka.

Takunkumin na man fetur daya ne kawai daga cikin matakan da kungiyar hadin kan Turai da Amirka suke dauka kan Iran. Sauran matakai sun hada har da hana musayar kudade ko kayaiyaki tsakanin suda Iran, abin da a sakamakon haka, darajar kudin Iran din ya fadi.

EU foreign policy chief Catherine Ashton takes part in the high-stakes talks on the controversial Iranian nuclear programme in Moscow, on Monday, June 18, 2012. Negotiators from Iran and world powers started today crunch talks in the Russian capital seen by some commentators as a final chance to solve the crisis diplomatically. (Foto:Kirill Kudryavtsev, pool/AP/dapd)
Kakakin harkokin waje ta kungiyar EU, Catherine AshtonHoto: AP

Kamar dai a da can, a wannan karo ma, Iran ta nuna cewar tana da wasu hanyoyi na kaucewa wannan takunkmi. Jiragen ruwan daukar man fetur wadanda kafin takunkumin suke zirga-zirga karkashin tutar kasar, yanzu suna jigila ne tareda tutar tsibirin Tuvalu. Iran din kuma tana iya amfani da wani bututun man fetur da ya ratsa Masar domin kaucewa takunkumin na kasashen Turai. Duk da haka, farashin man fetur ya fadi da misalin kashi 30 cikin dari, amma masana suka ce idan har tattalin arzikin kasashen na Amirka da Turai yaci gaba da bunkasa, tilas su koma ga Iran domin neman man fetur da suke bukata.