1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron hadin kan Turai kan Ukraine

Lateefa Mustapha Ja'afar ZMA
June 1, 2023

Kasashen nahiyar Turai na wani taro a Moldova, a wani mataki na nunawa kasar Rasha hadin kai shekara guda bayan da ta mamaye makwabciyarta Ukraine.

https://p.dw.com/p/4S5F0
Moldau Republik Treffen Ursula von der Leyen und Präsidentin Maia Sandu
Ursula von der Leyen da shugaba Maia Sandu ta MoldovaHoto: Andreea Alexandru/AP/picture alliance

Shugaban Ukraine din Volodymyr Zelenskyy ya ci gaba da mika kokon bararsa ga kasashen Turan kusan 50, a taron da ya mayar da hankali wajen nuna hadin kan Turai a yayin da Rasha ke tsaka da yakar Ukraine din.

Taron na gamayyar 'yan siyasar kasashen nahiyar Turai da ya hada baki dayan shugabannin kasashen nahiyar 47 in ban da na Rasha da takwaransa na Belarus, ya mayar da hankali ne kacokan kan alakarsu da Moscow sakamakon mamayar da ta yi a Ukraine shekara guda da ta gabata.

Baki dayan kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU 27, na son shawo kan kasashen gabashin Turai masu yawa da suka kwashe shekaru karkashin tsohuwar Tarayyar Soviet ko kuma tasirinta domin su hada hannu wajen mayar da martani kan karfa-karfar Rasha.

Reublik Moldau | Europagipfel in Bulboaca | Selenskyj, Vucic, Bettel, Berset
Vucic da Selenskyj da Bettel da BersetHoto: Ludovic Marin/AFP/Getty Images

Ana dai ganin sun zabi gudanar da taron a Maldova ne, domin isar da zazzafan sako ga Kremlin daga kungiyar Tarayyar Turai EU da kuma ita kanta Maldovan da ke goyon bayan kasashen Yamma da kuma ta karbi takardar takarar shiga kungiyar ta EU tare da takwararta Ukraine a watan Yunin bara. Da take jawabi a wata tattaunawa da ta yi da Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine a gefen taron, shugabar Moldovan Maia Sandu ta mika godiyarta ga makwabciyar tata Ukraine tana mai cewa:

"Ukraine ce ta bai wa Moldova kariya, muna matukar godiya kan hakan. Moldova na girmama iko da 'yanci da kuma jajircewar Ukraine. Moldova na goyon bayan tsarin sulhun da shugaban Ukraine ya fitar, kuma muna goyon bayan tsarin samar da kotun kasa da kasa ta musamman domin hukunta wadanda suka aikata laifuka da karfa-karfa a Ukraine."

A nasa bangaren shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya jaddada tallafin Turai ga Ukraine, inda ya ce:

Estland | Bundeskanzler Scholz in Tallinn
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

"Yana da matukar muhimmanci a gare mu mu taimaki Ukraine, kuma muna yin hakan. Turai ta hade waje guda domin taimakon Ukraine a fannin tsaron kasarta, kuma Jamus na bayar da taimako gaya. Abin da muka bayar ta fannin tsaron sararin samaniya na da matukar muhimmanci, a yayin da ake yawaitar samun hare-haren rokoki da na jiragen yaki daga Rasha. Tallafinmu shi ne, mu kare Ukraine daga gaza bai wa kanta kariya. Mun san cewa tilas a tabbatar da samun zaman lafiya bayan yaki, Jamus za ta bayar da gudunmawarta. Yadda hakan za ta kasance, abu ne da za mu tattauna nan gaba kuma muna tattaunawa akai junanmu da jimawa."

Sai dai duk da wannan kokari na kasashen Turan, Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine din na ci gaba da mika kokon bararsa kan su tallafa masa da karin makamai. Koda yake babbar bukatarsa ita ce ta shiga cikin kungiyar tsaro ta NATO, kamar yadda yake cewa:

"Mun tattauna kan dangantakarmu, har ma da batun kayan more rayuwa da ayyukan da suka fi muhimmanci da za mu nan ba da jimawwa ba. Babban abin da ya fi muhimmanci, shi ne makomarmu a EU. Ukraine a shirye take ta shiga cikin kungiyar tsaro ta NATO, muna jiran kungiyar ta shirya karbar mu. A ganina tabbatar tsaro abu ne mai matukar muhimmanci, ba ga Ukraine kadai ba har ma da makwabtanmu saboda karfa-katfar Rasha a Ukraine da ma yiwuwar bazuwar hakan zuwa sauran sassan Turai."

Norwegen | Jens Stoltenberg NATO Außenministertreffen in Oslo
Jens Stoltenberg, babban sakataren NATOHoto: Hanna Johre/NTB/REUTERS

A jawabinsa shugaban kungiyar tsaron ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana cewa, Moscow ba za ta iya hana Ukraine shiga cikinsu ba. Sai dai kuma akawai rarrabuwar kawuna tsakanin kasashe mambobin kungiyar kan shigar Kyiv NATO din, kwanaki kalilan kafin lokacin taronsu a tsakiyar watan Yuli mai zuwa a Vilnius.

Tun dai a shekara ta 2008 kungiyar ta NATO ta amince cewa sannu a hankali Ukraine za ta shiga cikinta, sai dai a yanzu suna taka-tsan-tsan. A yayin da Ukraine da kawayenta na gabashin Turai ke fatan a yi wani abu kan batun, kasashen Yamma kamar Amurka da Jamus na fargabar hakan ka iya kawo su kusa da yaki tsakaninsu da Rasha.