EU ta jaddada kudirin rage dogaro kan Rasha
March 25, 2022Talla
Rikici tsakanin Rasha da Ukraine ya kara zama matashiya ga kungiyar tarayyar Turan ta zama mai dogaro da kanta.
Kungiyar mai mambobin kasashe 27 ta jima ta na nazarin yadda za ta dogara da kanta a fannoni da dama tun bayan bullar annobar Corona da ta kawo nakasu ga muhimman abubuwan da tarayyar turai ke bukata kamar magunguna da microchips.
Shugabannin kungiyar ta EU suka ce tarayyar turai za ta yi kokarin samawa kanta mafita ta makamashinn gas da mai da kwal da kayayyakin sarrafawar masana'antu da kuma Alkama.
Shugabar hukumar tarayyar Turan Ursula von der Leyen ta ce hukumar za ta yi kokarin samar wani ingantaccen shiri daga nan zuwa tsakiyar watan Mayu domin daina dogaro akan mai da iskar gas da kuma kwal daga Rasha cikin shekaru biyar.