EU ta jinginar da batun sanya wa Rasha sabbin takunkumai
February 9, 2015Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar tarayyar Turai sun ce ba za a kakaba wa Rasha sabbin takunkumai yanzu ba. A wani taron da suka yi a birnin Brussels ministocin sun ce ya kamata a jira sakamakon taron kolin da zai gudana wannan Larabar a birnin Minsk na kasar Belarus, inda shugabannin kasashen Rasha da Ukraine da Jamus da kuma Faransa za su duba batun tsagaita bude wuta a rikicin gabashin Ukraine. Frank-Walter Steinemeier shi ne ministan harkokin wajen Jamus cewa yayi.
"Ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron birnin Minsk. Muna fata taron zai gano bakin zaren warware batutuwan da ke hana ruwa gudu."
Sai dai da farko ministocin sun amince a kara sunayen wasu mutane 19 a jerin wadanda EU ta sanya wa takunkumi. Ana zarginsu da tallafa wa 'yan aware magoya bayan Rasha a gabashin Ukraine.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Suleiman Babayo