1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta kai daukin kashe gobara a Girka

Abdullahi Tanko Bala
August 4, 2021

Ma'aikatan kwana kwana da kayan kashe gobara daga kasashen EU sun kai dauki Girka da Italiya da Albania da kuma arewacin Macedonia domin taimakawa wajen kashe gobarar daji a yankunan.

https://p.dw.com/p/3yXzp
Waldbrände in Griechenland
Hoto: Michael Pappas/AP Photo/picture alliance

Kwamishinan kungiyar tarayyar Turai mai kula da tallafi kan iftila'in annoba Janez Lenarcic ya ce suna aiki ba dare ba rana domin an kai dauki ga dukkan kasashen da ke fama da bala'in gobara a fadin nahiyar Turai. Yace an shirya jiragen sama na kasher gobara domin kai dauki.

Kwanaki takwas kenan a jere kasar Girka ke fama da wutar daji da ta mamaye wurare da dama ciki har da birnin Athens inda gidaje da dama da harkokin kasuwanci suka kone kurumus.

A farkon wannan makon ma kungiyar tarayyar Turai ta kai dauki Turkiya domin taimakawa kashe gobarar daji