1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta kakaba wa Iran sabon takunkumi

October 15, 2012

Ministocin harkokin wajen EU sun kakaba wa Iran karin takunkumi a ci-gaba da takaddamar da ake yi akan shirinta na nukiliya

https://p.dw.com/p/16QVz
Hoto: picture alliance/ZUMA Press

An jiyo ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle na mai cewa wannan shawara da aka tsayar a Luxembourg ta kuma hada ne da haramcin yin kasuwanci na dan gajeran lokaci da kamfanonin kasar ta Iran. Kafin tsai da wannan shawara ana aiki ne da haramcin akan ayyuka na lokaci mai tsawo. Sharuddan da aka gindaya a can baya su ba d ikon turawa da kuma turo kudi daga wasu bankunan Iran. To amma sabon takunkumin ya tanadi haramcin yin harka da wasu ma'aikatun kudi na Iran guda 34. An kuma sa haramcin sayen danyun kayan aiki kamar karfen samfulo da kuma bakar darma. A baya ga kuma haramcin sayen man fetur daka kasar ta Iran an kuma sa haramcin sayen iskar gas daga wannan kasa da da ma babu wannan harka tsakaninta da Kungiyar Tarayyar Turai(EU).

Mawalllafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu