1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta kakaba takunkumi karo na 6 kan Rasha

Abdullahi Tanko Bala
June 2, 2022

Kasar Hungary ta nemi kawo cikas ga sabbin takunkumin kungiyar tarayyar Turai kan kasar Rasha

https://p.dw.com/p/4CDc4
Russland | Präsident Putin und Patriarch Kirill
Hoto: Mikhail Metzel/Sputnik/Kremlin Pool Photo/AP/picture alliance

Jakadun kungiyar tarayyar Turai sun tsame shugaban cocin Orthodox na Rasha daga cikin sabbin takunkumin da kungiyar ta kakaba wa Rasha bayan ja-inja da kasar Hungary wadda ta yi barazanar yi wa kunshin takunkumin kafar ungulu.

Kasashen kungiyar ta EU dai sun amince ne da wasu jerin sabbin takunkumi akan Rasha bisa mamayar da ta yi wa kasar Ukraine.

Jerin takunkumin karo na shidda sun kunshi kwarya kwaryar haramcin shigo da mai da kuma cire bankin Sberbank na Rasha daga tsarin SWIFT na hada hadar kudade tsakanin kasa da kasa.

A yanzu shugabannin kasashen turan 27 suna da lokaci zuwa ranar Juma'a su amince da takunkumin a rubuce.