Ilham Tohti ya samu babbar lambar yabo daga EU
October 24, 2019Talla
A wani mataki na cigaba da matsin lamba ga gwamnatin China kan wani dan fafitika da ke tsare a gidan yari, kungiyar EU ta kuma bukaci gwamnatin Beijin da ta gaggauta sako dan fafitikar daga yari.
A shekarar 2014 ne gwamnatin China ta kama Ilham Tohti kan yadda yake caccakar tsarinta kan al'ummar Xinjian da ke Arewa maso yammacin kasar, an kuma yanke masa hukuncin daurin rai da rai.