Jami'an Turai sun taya Birtaniya murna
October 24, 2022Talla
Manyan jami'an kungiyar Tarayyar Turai biyu sun taya Rishi Sunak murna kan shirin zama sabon firaministan kasar Birtaniya na gaba bayan lashe kujerrar shugabancin jam'iyyar Conservative mai mulki tare da fata kan iya daidaita lamuran kasar.
Shi dai Rishi Sunak wanda zai zama sabon firaministan Birtaniya ya kasance tsohon ministan kudin kasar, kuma zai zama firaminista na biyar cikin shekaru shida da suka gabata, abin da ke nuna irin tsaka mai wuya na siyasa da aka shiga a kasar ta Birtaniya.